Isa ga babban shafi
Indonesia

Girgizar kasa ta hallaka sama da mutane 832 a Indonesia

Akalla mutane 832 sun rasa rayukansu, wasu kusan 540 suka jikkata, da dama suka bata, sakamakon girgizar kasar da ta afkawa garin Palu da ke tsibirin Sulawesi na kasar Indonesia a  ranar Juma’a.

Wani yanki na garin Palu, da ke tsakiyar tsibirin Sulawesi, da ke kasar Indonesia, Yau lahadi, 30, 2018.
Wani yanki na garin Palu, da ke tsakiyar tsibirin Sulawesi, da ke kasar Indonesia, Yau lahadi, 30, 2018. OLA GONDRONK / AFP
Talla

Girgizar kasar mai karfin maki 7.5 a ma’auninta na Ritcher, ta haddasa ambaliyar ruwa da ta kutsa cikin garin, kuma rahotanni sun ce, har ya zuwa safiyar yau, kasa ta cigaba da motsawa, lamarin da ya haddasa dagawar igiyar ruwa da tsawon mitoci biyu da ya sake antayawa garin na Palu.

Kasashen Duniya na ci gaba da jajintawa kasar,Faransa ta sanar da aikewa da jami'an agaji zuwa Indonesia.

Kakakin hukumar bada agajin gaggawa na Indonesia, Sutopo Nugroho, ya ce mafi akasarin mutanen da aka gano gawarwakinsu a warwartse, sun hallaka ne, sakamakon gine-ginen da suka fada musu.

A watan Agustan da ya gabata girgizar kasa ta hallaka mutane 500 a tsibirin Lombok na kasar ta Indonesia, inda ta rusa daruruwan gidaje.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.