Isa ga babban shafi
Iran

Mutane 22 ne suka mutu a Iran bayan kwankwadar barasa

Rahotanni daga kasar Iran sun ce akalla mutane 22 suka sheka lahira sakamakon kwankwadar gurbatacciyar giya.Bayanai sun ce duk da hukunci mai tsanani kan masu shan giya tun bayan juyin juya halin Islaman da akayi a shekarar 1979 har yanzu ana shigar da giya kasar ta barauniyar hanya, kana kuma ana girka ta gargajiya.

Barasa da ake shigowa da ita a kasar Iran
Barasa da ake shigowa da ita a kasar Iran ©Le Muscadier
Talla

Alkaluman da aka gabatar sun ce mutane 16 suka mutu sakamakon shan giyar a birnin Bandar Abbas dake gabar teku, yayin da aka kwantar da 168 a asibiti, kamar yadda shugaban yan sandan garin Esmail Mashayekh ya sanar.

Rahotanni sun ce an sake samun matsalar a yankin Alborz da Arewacin Khorzan inda aka samu rasa rayuka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.