Isa ga babban shafi
Afghanistan

Dan kunar bakin wake ya tarwatsa taron siyasa

Akalla mutane bakwai sun rasa rayukansu a wani harin kunar bakin wake da aka kaddamar kan jama’ar da ke taron yakin neman zabe a Afghanistan.

Dan kunar bakin wake ya tarwatsa kansa a tsakiyar jama'ar da ke taron yakin neman zabe a Afghanistan
Dan kunar bakin wake ya tarwatsa kansa a tsakiyar jama'ar da ke taron yakin neman zabe a Afghanistan DR
Talla

Hukumomin kasar sun ce, mutane 25 sun samu rauni a harin wanda dan kunar bakin waken ya tarwatsa kansa a tsakiyar jama’ar da ke goyon bayan dan takarar Majalisar Dokoki, Abul Nasir Mohmmand.

Wasu daga cikin masu raunin na cikin mawuyacin hali kamar yadda mai magana da yawun gwamnan lardin Nangarhar, Ataullah Khogyani ya bayyana.

An dai shirya gudanar da zaben na ‘yan Majalisar Dokoki a ranar 20 ga watan Oktoba.

Hukumar Zaben Kasar Mai Zaman Kanta ta ce, akalla ‘yan takara biyar aka hallaka a hare-haren da aka kaddamar a baya-bayan a Afghanistan.

Da ma dai, kungiyoyin Taliban da IS sun lashi takobin haddasa matsaloli ga shirye-shiryen gudanar da zaben, yayin da suka zafafa hare-hare a sassan kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.