Isa ga babban shafi
Turkiya-Saudiya

Saudiya ta aike da wakilai a Turkiya

Wata tawaga daga Saudiyya ta isa Turkiyya a yau Juma’a don tattaunawa kan fitaccen dan jaridan nan da ya bace bayan ya shiga ofishin jakadancin Saudiyyar dake Istambul a makon da ya gabata.

Jamal Khashoggi dan jaridar Saudiya da ya bace bayan shiga ofishin kasar Saudiya a Turkiya
Jamal Khashoggi dan jaridar Saudiya da ya bace bayan shiga ofishin kasar Saudiya a Turkiya Middle East Monitor/Handout via REUTERS
Talla

Ziyarar wannan tawaga na zuwa ne dangane da dambarwar dake ci gaba da kamari, bayan jaridar Washington Post ta ruwaito cewa Turkiya na da hotunan bidiyon da ke tabbatar da cewa an gana wa Jamal Khasogghi azaba har sai da ya ce ga garinku nan a ofishin jakadancin Saudiya.

Batu dai ba kawai zai ci gaba da lalata dangantaka tsakanin Turkiya da Saudiya bane, zai ma shafi kimar Saudiyar da Yerima mai jiran gado Mohammed bin Salman a idanu manyan kasashen Duniya.

A ranar 2 ga watan Oktoban nan ne, dan jaridar dake yawan bayyana ra’ayinsa a jaridar Washington Post, Jamal Khasogghi ya shiga ofishin jakadanci, don karbar wasu takardu gabanin aurensa amma ya bace .

A halin da ake ciki, wasu majiyoyi na gwamanatin Turkiya na cewa, ‘yan sanda sun yi amannan cewa kasheshi aka yi, amma Saudiya ta musanta haka.

Ana sa ran wannan tawagar ta Saudiya, wacce ba a tantance wadanda ke cikinta ba, za ta gana da jami’an Turkiya a cikin ranakun karshen makon nan, kamar yadda kafofin yada labaran kasar suka sanar a yau Juma’a.

Shugaban Faransa Emmmanuel Macron yan lokuta da kamala taron Francophonie ya bayyana cewa bacewar Khashoggi ba abin wasa bane, yana mai kira da a gudanar da bincike don samun haske kan lamarin mai matukar daure kai.

Sai dai Shugaba Macron ya ce har yanzu bai tuntubi sarki Salman na Saudiyya ko dan sa Yerima mai jiran gado, Mohammed bin Salman dangane da wannan rikici.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.