Isa ga babban shafi
Afganistan-Zabe

An shiga rana ta biyu da fara zaben 'yan majalisu a Afghanistan

An ci gaba da kada kuri’u a rana ta biyu da fara zaben ‘yan majalisu na Afghanistan bayan hare-haren jiya Asabar da za suka haddasa hargitsi a wasu runfunan zaben.

Zaben na yau na zuwa ne bayan hare-haren jiya Asabar da ya hallaka kusan mutane 20 baya ga jikkata wasu 170.
Zaben na yau na zuwa ne bayan hare-haren jiya Asabar da ya hallaka kusan mutane 20 baya ga jikkata wasu 170. 路透社
Talla

Zaben wanda ke zuwa watanni 6 gabanin zaben shugaban kasa rahotanni na nuni da cewa kusan kowanne yanki na fuskantar karancin kayakin aiki baya ga rashin isarsu akan lokaci.

Rahotanni sun ce gwamnati ta kara yawan jami’an da ke bayar da tsaro a rumfunan zaben inda yawansu yanzu ya tasamma dubu 50 yau Lahadi bayan hare-harenm jiya da suka hallaka kusan mutane 20 baya jikkata wasu 170.

Hukumar zaben Afghanistan ta ce fiye da mutane miliyan 3 cikin mutane miliyan 8 da daubu dari takwas da ake saran su kada kuri’ane suka samu zarafin kada kuri’unsu a jiya Asabar, yayinda ayau Lahadi kuma aka bude rumfunan zabe 401 bisa tsattsauran tsaro.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.