Isa ga babban shafi
Syria

Taron kasashe 4 ya cimma matsayar magance rikicin Syria a siyasance

Shugabannin Turkiya, Rasha, Faransa da kuma Jamus, da suka gana a birnin Istanbul, sun cimma matsayar warware yakin basasar Syria a siyasance.

Shugaban Rasha Vladimir Putin, da takwarorinsa Emmanuel Macron na Faransa, Angela Merkel ta Jamus da kuma mai masaukin baki shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan a birnin Istanbul yayin ganawa kan warware rikicin kasar Syria.
Shugaban Rasha Vladimir Putin, da takwarorinsa Emmanuel Macron na Faransa, Angela Merkel ta Jamus da kuma mai masaukin baki shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan a birnin Istanbul yayin ganawa kan warware rikicin kasar Syria. AFP/Murat KULA
Talla

Shugabannin sun kuma amince da ci gaba da wanzuwar yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma cikin watan da ya gabata a lardin Idlib, yanki na karshe dake hannun ‘yan tawayen kasar.

An dai shafe sa’o’i ana ganawa tsakanin Recep tayyib Erdogan, Emmanuel Macron, Angela Merkel da kuma Vladmir Putin, kan yadda za’a kawo karshen yakin Syria wanda ya shiga shekara ta 7 da barkewa, zuwa yanzu kuma yayi sanadin hallakar sama da mutane 360,000.

Bayan kammala ganawar ce, mai masaukin baki shugaban Turkiya Erdogan, ya kara da cewa, za’a kafa wani kwamiti na musamman, da zai samar da sabon kundin tsarin mulkin Syria kafin karshen wannan shekara, abinda zai bada damar gudanar da sahihin zabe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.