Isa ga babban shafi
Amurka

Amurka ta maidawa Iran takunkuman da aka cire mata

Gwamnatin Amurka ta ce takunkuman karya tattalin arzikin da ta maida kan Iran, wadanda za su soma aiki a Litinin 5 ga watan Nuwamba, 2018, za su shafi mutane, hukumomi da kamfanoni akalla 700.

Shugaban Amurka Donald Trump.
Shugaban Amurka Donald Trump. REUTERS/Joshua Roberts
Talla

Amurka ta ce takunkuman kai tsaye za su shafi sassan tattalin arzikin Iran da suka hada da bankuna, kamfanonin sufurin jiragen ruwa, da kuma sashin hakar danyen man fetur na kasar.

Matakin sake kakabawa Iran takunkuman ya zo ne watanni 6, bayanda shugaba Donald Trump ya janye Amurka daga yarjejeniyar nukiliya 2015 da Iran ta cimma tsakaninta da manyan kasashen duniya, ciki har da Amurkan.

Tun bayan daukar matakin ne Trump ya soma aikin maido da takunkuman karya tattalin arzikin da tsohon shugaban Amurka Barrack Obama ya janyewa Iran, wadda zai kammala a ranar Lahadi nan mai zuwa cikin dare.

Yayinda yake karin bayani akan matakin, sakataren harkokin Amurka Mike Pompeo ya ce takunkuman ba za su shafi kasashe guda 8 ba, wadanda bai kai ga bayyana sunayensu ba.

Sai dai ana kyautata zaton daga cikin kasashen akwai India, Japan, Korea ta Kudu da kuma China, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya rawaito.

Pompeo ya kara da cewa sun zaratas da matakin ne domin dakile tattalin kudaden da kasar ke amfani da su wajen inganta fasaharta kan makamashin Uranium domin kera makaman nukiliya da marawa ta’addanci baya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.