Isa ga babban shafi
Iraqi

IS ta gina manyan kaburbura sama da 200 a Iraqi - MDD

Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da gano manyan kaburbura sama da 200, wadanda ta ce mayakan IS sun bari a yankunan da suka taba mamayewa a Iraqi.

Daya daga cikin manyan kaburburan da ake zargin cewa mayakan IS sun binne gawarwakin 'yan kabilar Yazidi da suka yiwa kisan gilla, a arewa maso yammacin yankin Sinjar dake Iraqi. 3/2/2015.
Daya daga cikin manyan kaburburan da ake zargin cewa mayakan IS sun binne gawarwakin 'yan kabilar Yazidi da suka yiwa kisan gilla, a arewa maso yammacin yankin Sinjar dake Iraqi. 3/2/2015. AFP/File
Talla

Majalisar ta ce kaburburan da aka kiyasta na dauke da gawarwakin mutane dubu 12,000, babbar shaida ce, kan laifukan yakin da mayakan na IS suka tafka.

Ofishin majalisar dinkin duniyar dake Iraqi ya ce an gano kaburburan guda 202 ne a wasu yankuna da suka kasance a karkashin mamayar mayakan IS daga shekarun 2014 zuwa 2017, a yammaci da arewacin kasar, zalika rahoton yayi gargadin da akwai yiwuwar sake gano wasu karin manyan kaburburan.

Rahoton majalisar dinkin duniyar ya ce an gano kusan rabin kaburburan  ne a lardin Nineveh, inda a nan ne mayakan IS suka yiwa ‘yan kabilar Yazidi kisan gilla hadi da azabtar da dubbansu.

Ragowar manyan kaburburan kuwa, an gano su ne a wasu yankunan arewacin Iraqi da suka hada da Kirkuk, Salaheddin da kuma Anbar.

A watan Agustan da ya gabata, wata tawagar kwararru ta majalisar dinkin duniya, suka soma bincike da tattara shaidu kan zarge-zargen aikata laifukan yaki, da suka hada da zabatarwa da kuma kisan kare dangi, domin mikawa kotunan kasar Iraqi, wadanda za su yi amfani da su yayin yanke hukunci kan mayakan IS da ake yiwa shari'a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.