Isa ga babban shafi
Indonesia

An kammala binciken wadanda suka mutu a hadarin jirgin Indonesia

Kasar Indonesia ta sanar da kawo karshen binciken da ta ke na gano sauran fasinjojin jirgin Lion Air da ya yi hadari dauke da mutane 189 gab da tekun Java fiye da makwanni biyu da suka gabata.

Kawo yanzu dai gawar mutane 79 aka iya ganowa daga cikin Pasinjojin 189 ko da dai an gano sassan jikin wasu daga cikinsu.
Kawo yanzu dai gawar mutane 79 aka iya ganowa daga cikin Pasinjojin 189 ko da dai an gano sassan jikin wasu daga cikinsu. REUTERS/Stringer
Talla

Bayan gano wasu jakunkuna 196 dauke da sassan jikin dan adam tare da kuma da gawar mutane 79 da aka mika su ga iyalansu don binnewa, shugaban tawagar masu binciken Muhammad Syaugi ya ce an kawo karshen binciken la’akari da yadda aka gaza gano komi tun daga jiya Juma’a.

Muhammad Syaugi ya nemi yafiyar iyalan wadanda aka gaza gano ‘yan uwansu, yayinda ya ce sun kammala ka iwa iyakar inda za su iya a binciken.

Kawo yanzu dai an gaza gano dalilin da ya haddasa hadarin jirgin yayinda kamfanin na Lion Air zai biya diyyar dala dubu dari da 3 kan kowanne pasinja da ya rasa ransa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.