rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Pakistan Ta'addanci

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Fiye da mutane 30 sun mutu a harin kunar bakin waken Pakistan

media
Tuni dai kungiyar Amnesty international ta yi tir da harin wanda ta kira da tsabagen rashin darajanta rayukan bil’adama. REUTERS/Mohammad Ismail

Akalla mutane 31 suka mutu yayinda wasu fiye da 50 suka jikkata sakamakon wani harin kunar bakin wake yau a kasuwar garin Kalaya mai cike da jama’a da ke yankin Orakzai na arewa maso yammacin Pakistan mai yawan mabiya Shi’a.


Rahotanni sun ce galibin wadanda harin ya rutsa da su mabiya shi’a ne lokacin da su ke tsaka da hada-hadar saye da sayarwa a kasuwar wadda ta shahara wajen sayar da kayan lambu da na marmari.

Wasu ganau sun ce kafin tashin Bomb din an ga wani kankanin yaro haye a babur da fuskarshi a rufe ya shiga cikin kasuwar da kwali a bayan sa wanda kuma ake kyautata zaton a ciki aka sanyo bom din wanda ya hallaka tarin jama’a tare da jikkata fiye da 50.

Babban jami’I mai kula da harkokin tsaro na garin Kalaya Khalid Iqbal, ya ce tuni aka isar da wadanda suka raunata a harin asibitin Kyber Pakhtunkhwa ciki har da 17 da ke cikin matsanancin hali.

Tuni dai kungiyar Amnesty international ta yi tir da harin wanda ta kira da tsabagen rashin darajanta rayukan bil’adama.

Yankin Orakzai da ke gab da iyakar kasar ta Pakistan da Afghanistan na daga cikin yankuna 7 na kasar da hare-haren ta’addanci ya tagayyara yayinda tsohon shugaban Amurka Barrack Obama ya bayyana shi da mafi hadarin waje a doron kasa.