Isa ga babban shafi
Syria

Syria na zargin 'Yan tawayen kasar da kai harin guba

Gwamnatin Syria ta zargi ‘yan ta’adda da kaddamar da harin iska mai guba, lamarin da ya yi sanadiyar kwantar da mutane kimanin 100 a asibiti bayan sun gaza numfashi, yayin da kasar Rasha ta kai wa ‘yan ta’addan hare-haren jiragen sama.

Kamfanin Dillancin Labaran kasar, SANA ya rawito cewa, mutane 107 ne suka fuskanci wahalar numfashi, yayin da wani jamai’in kiwon lafiya, Ziad Hajj ya ce, akwai alamar sinadarin Chlorine aka yi amfani da shi a harin.
Kamfanin Dillancin Labaran kasar, SANA ya rawito cewa, mutane 107 ne suka fuskanci wahalar numfashi, yayin da wani jamai’in kiwon lafiya, Ziad Hajj ya ce, akwai alamar sinadarin Chlorine aka yi amfani da shi a harin. George OURFALIAN / AFP
Talla

An kaddamar da harin iskar gas din ne a birnin Aleppo da ke karkashin ikon dakarun gwamnatin Syria kamar yadda gwamnati da kungiyar da ke sa ido a kasar mai cibiya a Birtaniya ta sanar.

Rasha ta zargi masu ikirarin Jihadi da kai harin na sinadarin Chlorine, abin da ya sa ta kaddamar da harinta na farko cikin tsawon watanni kan tungar mayakan da ke wajen birnin Aleppo.

Kamfanin Dillancin Labaran kasar, SANA ya rawito cewa, mutane 107 ne suka fuskanci wahalar numfashi, yayin da wani jamai’in kiwon lafiya, Ziad Hajj ya ce, akwai alamar sinadarin Chlorine aka yi amfani da shi a harin.

Wani wakilin Kamfanin Dillancin Labaran Faransa da ya kware a fannin daukan hotuna yace, ya ga gomman fararen hula da suka hada da maza da mata na tururuwa zuwa asibitin Aleppo, in da wasu aka tura su a gadon marasa lafiya, yayin da kuma aka sanya musu na’urar shakar numfashi a hanci.

Wannan dai shi ne zargi na baya-baya nan kan amfani da sinadarin Chlorine wajen kai hare-hare a yakin shekarun 7 da ya lakume rayuka sama da dubu 360 a Syria tare da raba miliyoyin jama’a da muhallansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.