rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Majalisar Dinkin Duniya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Kungiyar kwadago ta duniya ta koka da yadda albashin maza ya zarta na mata

media
Kungiyar ta ce a wasu kasashe mata sun fi maza ilimi amma kuma abin takaici shine ba’a basu albashin da ya dace da su. REUTERS/Gonzalo Fuentes/Pool

Kungiyar Kwadago ta duniya ta ce an samu raguwar yadda ake karin albashin ma’aikata a shekarar 2017 irin sa na farko tun bayan shekarar 2008 da duniya ta fuskanci matsalar koma bayan tattalin arziki.Wannan na daga cikin rahotan kungiyar kula da kwadago ta Majalisar Dinkin Duniya.


Sabon rahotan kungiyar kwadago ta duniya ya bayyana cewar har yanzu ana biyan mata albashi kasa da maza da ya kai kashi 20 daga cikin dari, duk da bukatar daidaito da akeyi.

Alkaluman da kungiyar ta gabatar ya ce binciken da aka gudanar a kasashe 136, albashin ma’aikata ya ragu daga kashi kusan biyu da rabi zuwa kusan kasha biyu.

Kungiyar tace albahsin ma’aikata a kasashe masu tasowa da kuma kasashen G20 da arzikin su ke habaka ya ribanya har sau uku idan aka kwatanta da shekaru 20 da suka gabata.

Darakta Janar na kungiyar Guy Ryder ya bayyana banbancin albashin da ake samu tsakanin maza da mata a matsayin babban rashin adalci, inda ya bukaci kasashen da su tashi tsaye wajen gyara al’amarin.

Kungiyar ta ce a wasu kasashe mata sun fi maza ilimi amma kuma abin takaici shine ba’a basu albashin da ya dace da su.