rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Afghanistan

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Taliban ta kashe mutane sama da 10 a wani harin kunar bakin wake

media
shugaban kasar Afghanistan Ashraf Ghani UNAMA News

Kungiyar Taliban a Afghanistan ta dauki alhakin kai harin kunar bakin wake a kusa da wani ofishin kamfanin tsaro na Birtaniya mai zaman kansa a Kabul wanda yayi sanadiyar hallaka akalla mutane 10. Ma’aikatar cikin gida da Yan Sanda sun ce wani bam ne ya tashi a cikin wata mota kusa da ofishin.


Wahid Majroh, mai Magana da yawun ma’aikatar lafiyar, ya tabbatar da mutuwar mutane 10, yayin da 19 suka jikkata.

Shima mataimakin kakakin ma’aikatar lafiya Nasrat Rahimi ya tabbatar da adadin, sai da yace yana iya karuwa.

A dai gefen kuma Shugaban kasar Afghanistan Ashraf Ghani ya sanar da sunayen mutane 12 karkashin jagorancin shugaban ma’aikata Abdul Salam Rahimi a matsayin tawagar da za ta wakilci gwamnatir kasar a tattaunawa da kungiyar Taliban.

A wani taron zaman lafiyar kasar Afghanistan da ya gudana a Geneva, gwamnatin da Jami’an Diflomasiyyar kasashen yammacin duniya dama Majalisar Dinkin Duniya sun nuna bukatar ganin an kawo karshen yakin kasar na shekaru 17,

Tuni dai wasu suka fara kallon yunkurin na Ashraf Ghani a matsayin gazawa, maimakon ci gaba da yakar kungiyar ta Taliban.