Isa ga babban shafi
Syria

Kurdawan Syria sun nemi ceton Faransa daga farmakin Turkiya

Kurdawan kasar Syria sun bukaci Faransa da ta basu taimakon gaggawa na diflomasiya da soji, domin kare kansu ga barazanar fuskantar farmakin sojin kasar Turkiya.

Wani sojin Amurka tare da daya daga cikin mayakan Kurdawa na kungiyar YPG a Syria.
Wani sojin Amurka tare da daya daga cikin mayakan Kurdawa na kungiyar YPG a Syria. AFP/File/DELIL SOULEIMAN
Talla

Neman agajin da mayakan Kurdawan na kungiyar YPG, na zuwa ne bayan da a ranar Laraba, shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana shirin janye dakarunsa da ke baiwa Kurdawan gowon baya wajen yakar kungiyar ISIS a arewacin Syria

Janyewar sojin Amurka daga Siriya na iya haifar da tsaiko ga kokain murkushe mayakan ISIS da Kurdawan ke yi.

A halin yanzu dai akalla dakarun Amurka 2000 ke cikin Syria, wadanda ke taimakawa mayakan Kurdawa na YPG wajen yakar kungiyar ISIS, sai dai Turkiyya na kallon su a matsayin ‘yan ta’adda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.