Isa ga babban shafi
Japan

Japan za ta dawo da cinikayyar nau'in kifin Whale da duniya ta haramta

Kasar Japan ta ce, za ta dawo da cinikayyar manyan kifayen nan da ake kira Whale a turance nan da watan Yuli mai zuwa, al’amarin da ka iya janyo mata caccaka daga kasashen duniya.

Matakin Ficewar Japan daga Hukumar ta IWC na nuna cewa kai tsaye za ta dawo da kamun kifin tare da cinikayyarsa a duniya.
Matakin Ficewar Japan daga Hukumar ta IWC na nuna cewa kai tsaye za ta dawo da kamun kifin tare da cinikayyarsa a duniya. REUTERS/Anthony Phelps
Talla

Cikin bayanan gwamnatin ta Japan ta bakin kakinta Yoshihide Suga, ta ce za ta fice daga yarjejeniyar da ta cimma da Hukumar da ke Kare Kifayen na Whale a duniya IWC, bayan da ta yi zargin kame daruruwan nau'in kifayen cikin shekarun nan bisa fakewa da binciken Kimiyya.

A cewar Japan duk kasancewar, cin naman nau'in kifayen na daga cikin al’adunta amma yarjejeniyar ta shekarar 1986 ta sanya ta ci gaba da Haramtawa jama'arta kamawa ko ma cin kifin wanda.

Matakin Ficewar Japan daga Hukumar ta IWC na nuna cewa kai tsaye za ta dawo da kamun kifin tare da cinikayyarsa a duniya.

Yanzu haka dai Japan ta bi sahun kasashen Iceland da Norway wajen bijirewa yarjejeniyar ta shekarar 1986 karkashin IWC wajen halatta cinikayya da hada-hadar nau'in kifin, matakin da tuni ya fara haddasa ce-ce-ku-ce tsakanin kasashen da tun farko suka amince da haramcin.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.