Isa ga babban shafi
Bangladesh

Fira Ministar Bangladesh na neman zarcewa wa'adi na 4

Al’ummar Bangladesh na kada kuri’a a zaben shugaban kasar yau Lahadi, wanda Fira Minista Sheikh Hasina ke neman zarcewa bisa shugabancin kasar wa’adi na hudu.

Wasu ma'aikatan zabe a Bangladesh, yayin da aka soma kada kuri'a a zaben shugabancin kasar.
Wasu ma'aikatan zabe a Bangladesh, yayin da aka soma kada kuri'a a zaben shugabancin kasar. AFP / MUNIR UZ ZAMAN
Talla

Zaben wanda ke gudana cikin tsauraran matakan tsaro, ya zo yayin da kungiyoyin kare hakkin dan adam ke zargin gwamnatin Hasina da cin zarafin ‘yan adawa ta hanyar kama dubbansu.

Sai dai a gefe guda an yabawa shugabar kan jajircewarta wajen farfado da tattalin arzikin kasar, da kuma tallafawa dubban 'yan gudun hijirar kabilar Rohingya da suka tsere daga kasarsu Myanmar saboda kisan gillar da sojin kasar ke musu babu kakkautawa.

Mafi akasarin ‘yan adawar da ake zargin gwamnatin Hasina da tsarewa dai magoya bayan babbar abokiyar hamayyarta ne Khaleda Zia, wadda yanzu haka ke karkashin hukuncin zaman gidan yari na shekaru 17, kan zargin cin hanci da rashawa, matakin da Zia ke ci gaba da bayyana shi a matsayin bi ta da kullin siyasa.

Jami’an tsaro kimanin dubu 600 aka girke a sassan kasar, wadanda ke sa idanu kan rumfunan zabe dubu 40, domin dakile duk wani yunkurin tada rikici.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.