rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Yemen Saudiya Majalisar Dinkin Duniya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

'Yan tawayen Houthi sun kauracewa tattaunawar sulhu

media
Wasu mayakan 'yan tawayen Houthi a birnin Hodeida na kasar Yemen. REUTERS/Abduljabbar Zeyad

‘Yan tawayen Houthi da ke iko da kasar Yemen, sun kauracewa tattaunawar Sulhu da majalisar dinkin duniya ta jagoranta wannan Lahadi a birnin Hodeida.


‘Yan tawayen na Houthi sun zargi kwamitin Majalisar dinkin duniya mai sa ido kan yarjejeniyar tsagaita wuta a birnin na Hodeida, da kokarin aiwatar da wasu boyayyun manufofi na daban.

Kwamitin hadakar ya kunshi wakilan ‘yan tawayen Houthi, bangaren gwamnatin Yemen da Saudiya, sai kuma majalisar dinkin duniyar mai shiga tsakani.

Rahotanni sun ce ko a jiya Asabar, an yi artabu tsakanin mayakan na Houthi da sojojin gwamnati da Saudiya ke jagoranta, a birnin na Hodeida, lamarin da ke barazanar wargaza yejejeniyar sulhun da aka cimma a Sweden cikin shekarar bara, kan janyewar mayakan dukkan bangarorin daga birnin mai dauke da tashar ruwan da Yemen ta dogara kanta.

A watan Nuwamban shekarar bara, mutane akalla 149 suka mutu a kazamin fadan aka fafata tsakanin dakarun gwamnatin Yemen da 'Yan Tawayen Houthi a garin Hodeida.

Majiyar asibiti da sojin kasar, sun ce a cikin sa’oi 24 an kashe 'yan tawaye akalla 110, yayin da mayakan gwamnati 32 suka rasa rayukan su.