Isa ga babban shafi
Faransa

Sojin Faransa za su ci gaba da zama a Gabas ta Tsakiya - Macron

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce kasarsa za ta ci gaba da wanzuwa a yankin Gabas ta Tsakiya ta fuskar soji.

Shugaban Faransa Emanuel Macron, yayin ziyarar da ya kai sansanin sojin kasar da ke yankin kudanci, da ke garin Toulouse.
Shugaban Faransa Emanuel Macron, yayin ziyarar da ya kai sansanin sojin kasar da ke yankin kudanci, da ke garin Toulouse. REUTERS/Regis Duvignau
Talla

Macron ya bayyana matsayin gwamnatinsa ne a wannan Alhamis, yayin gabatar da jawabi a sassanin sojin kasar da ke kudancin Faransa, inda ya ce sojojin Faransa za su ci gaba da bada cikakkiyar gudunmawa ga sha’anin tsaron kasashen Yankin gabas ta Tsakiya daga farkon shekarar 2019 da muke ciki zuwa karshenta, duk da matakin Amurka na shirin janye dakarunta daga Syria.

A cewar shugaban na Faransa ci gaba da wanzuwar karfin dakarun kasar a Yankin, muhimmin abu ne dangane da cika alkawarin da aka dauka na kawo karshen ta’addancin kungiyar IS.

Tuni dai shugaba Macron ya soki matakin takwaransa na Amurka Donald Trump kan shirin janye dakarunsa daga Syria, bayan ikirarin nasarar murkushe mayakan IS, matakin da shugaban na Faransa ya bayyana a matsayin kaucewa daga kan manufar da manyan kasashen duniya ta tabbatar da zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya.

A halin yanzu dai Faransa na da sojoji dubu 1 da 200 a Yankin Gabas ta Tsakiya, wadanda ke baiwa sojojin Iraqi horo, yayinda wasunsu ke taimakawa wajen yakar kungiyar IS a Syria.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.