Isa ga babban shafi
Indonesia

Manoma a Indonesia sun shiga noma wani icce da aka ce ya na warkar duk wata cuta a duniya

A kasar Indonesia manoma wani nau’in icce da aka chamfa ganyensa da cewa, ya na maganin duk wata cuta a duniya, na chan suna ta rige-rige moma itacen don saidawa kasashen duniya. Masana dai sun ce babu gwaji da aka yi sosai domin tabbatar da ingancin itacen.

Ganyen itaciyar da aka ce tana warkar da duk  wata cuta a duniya
Ganyen itaciyar da aka ce tana warkar da duk wata cuta a duniya AFP
Talla

Itacen mai suna Kratom , mai shigen itatuwan ganyen shayi, an dade ana amfani dashi a kudu maso gabashin Asia da Papua New Guinea wajen rage dukkan radadin ciwo, da sa karsashi, to amma ayanzu haka an fara nika ganyen itacen ana saidawa a kasashen duniya kuma yana warkar da cutuka masu yawan gaske.

Ganin yadda mutane masu tarin yawa suka raja’a da shan ganyen itacen don magance masu dukkan wata cuta yasa jamian lafiya na zaman ke fargaban sa.

Wannan yasa aka haramta amfani da shi a cikin kasashen Indonesia, Malaysia da Thailand, amma kuma ba’a hana manoman itacen nomawa da kaiwa kasashen duniya ba.

Jamian lafiya a kasar Amurka wadda a yanzu haka tafi kowace kasa a duniya amfani da itace, kasancewar mutane akalla miliyan 5 basa iya yi saida itacen, na fargaban yadda wannan itace ya sami karbuwa.

Shi wannan itace an yarje mutane su yi amfani dashi a jihohi 43 na Amurka amma kuma jamian lafiya na kara matsin lamba don a rage amfani dashi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.