Isa ga babban shafi
Iran

An kashe sojin juyin juya halin Iran 27

Wani dan kunar bakin-wake ya hallaka sojin juyin juya halin Iran 27 a kudu maso gabashin kasar, yankin da ke fama da hare-haren ‘yan tawaye.

Wasu daga cikin sojin juyin juya halin Iran
Wasu daga cikin sojin juyin juya halin Iran AFP
Talla

Kungiyar Jaish al Adl ta ‘yan Sunni da ke fafutukar nema wa ‘yan kabilar Baluchi cikakken ‘yanci, ta dauki alhakin harin na ranar Laraba.

Tuni rundunar juyin juya halin ta gargadi makiyan kasar bayan kaddamar da wannan farmakin, in da take cewa, martaninta zai shafi hatta kasashen ketare.

Koda yake rundunar ba ta ambaci sunan makiyan karara ba, amma a can baya, Iran ta sha zargin Saudiya da nuna goyon baya ga ‘yan awaren Sunni a kasar, zargin da Saudiya ta musanta.

Dan kunar bakin-wake ya yi amfani da mota makare da bama-bamai wajen kaddamar da farmakin wanda ya raunta dakarun juyin juya halin 13.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.