India ta kai hare-haren jiragen sama kan Pakistan
Kasar India ta ce, ta kaddamar da hare-haren sama akan ‘yan tawayen yankin Kashmir da ke Pakistan, in da ta kashe da dama daga cikinsu.
Wallafawa ranar:
Gwamnatin India ta ce, dakarunta sun kai hare-haren ne kan sansanin horar da mayakan Kungiyar Jaish-e-Mohammad da ke Balakot, kuma hakan na zuwa ne wata guda da wani harin kunar bakin wake ya kashe sojojin India 46 a Kashmir.
Ministan Harkokin Wajen India, Vijay Gokhale ya shaida wa manema labarai cewa, daga cikin wadanda hare-haren saman suka hallaka har da kwamandojin ‘yan tawayen.
Matakin kaddamar da harin na baya-bayan nan ya kara nuna yadda kasashen biyu masu makaman nukiliya ke ci gaba da takun saka da juna.
Kaddamar da farmakin na zuwa ne bayan wata majiyar asiri ta ce, Kungiyar Jaish-e-Mohammad na shirin kaddamar da wani sabon harin kunar bakin wake a India.
karon farko kenan tun shekarar 1971 da ake kai harin sama a kan iyakar da ta raba kasashen biyu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu