Isa ga babban shafi
Syria

An tabbatar da zargin amfani da makami mai guba a Syria

Hukumar kula da haramcin amfani da makamai masu guba ta duniya OPCW, ta ce an yi amfani da makamai masu dauke da sinadarin Chlorine, a harin da aka kai kan birnin Douma da ke karkashin ‘yan tawaye a Syria.

Wani jariri da likitoci suka tabbatar da cewa ya shaki sinadarin Chlorine mai guba a garin Douma da ke Syria.
Wani jariri da likitoci suka tabbatar da cewa ya shaki sinadarin Chlorine mai guba a garin Douma da ke Syria. REUTERS/Bassam Khabieh
Talla

Rahoton, sakamakon bincike ne da hukumar ta OPCW ta gudanar, bayan tura tawaga zuwa inda aka kai harin a watan Afrilu na shekarar 2018, wanda shaidun gani da ido suka ce mutane 43 suka hallaka a sanadinsa.

Tuni dai Rasha da ke marawa gwamnatin Bashar al-Assad baya, ta yi watsi da rahoton, inda ta ce da tuggun aka shirya wajen kai harin da zummar shafawa gwamnatin bashar al-Assad bakin fenti.

Bayan dora alhakin harin kan gwamnatin Syria, Amurka da Birtaniya da kuma Faransa kaiwa sansanoni da kuma rumbunan ajiyar makaman sojin na Syria hare-hare. Sai dai har yanzu gwamnatin Syria na ci gaba da musanta zargin da ake mata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.