rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya
  • Palestinawa 22 hare-hare daga Israela ya kashe a Gaza.
  • Dan kunar bakin wake ya kashe mutun daya a ofishin 'yan sandan Indonesia
  • Yau ake zama a bainin jama'a game da tsige Shugaban Amurka Trump
  • Wasu 'yan kasar Kamaru sun shiga Otel da Shugaba Paul Biya ke ciki a Paris.
  • Tashin Bam a Kabul na Afghanistan ya kashe mutane 7
  • Saudiya, Daular Larabawa da Bahrain za su shiga wasannin kwallon kafa tare

Syria ISIL Iraqi

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Mayakan ISIS da dama sun mika kansu a Syria

media
Kauyen Baghouz da ke lardin Deir Al Zor a Syria, yanki mafi girma na karshe da ke karkashin ikon mayakan ISIS. REUTERS/Rodi Said

Hukumomin da ke sa ido kan yakin Syria, sun ce mayakan kungiyar ISIS masu yawa sun mika kansu, ga rundunar Kurdawan YPG da Amurka ke marawa baya.


Yawan mayakan na ISIS da suka zubar da makamansu ya kai 200, ya biyo bayan gagarumin farmakin da mayakan Kurdawan suka kaddamar kan kauyen Baghouz, yanki mafi fadi na karshe da ke karkashin ikon ISIS a Syria.

Mayakan na ISIS sun samu damar mika kansu ne, bayan da rundunar hadaka ta ‘yan tawayen Syria da mayakan Kurdawa suka sassauta hare-haren da suka kaddamar akansu, domin baiwa fararen hula damar ficewa daga yankin.

Har yanzu dai babu karin bayani kan yawan mayakan na ISIS da suka rage a cikin kauyen na Baghouz.

Duk da cewa ana gaf da murkushe ISIS a kasashen Syria da Iraqi, masana fannin tsaro sun bayyana cewa har yanzu mayakan kungiyar suna da sauran barazana, la’akari da hare-haren kunar bakin waken da suke kaiwa a manyan birane da kauyuka.