rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Kazakhstan

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Kazakhstan ta sauya sunan babban birninta

media
Nursultan Nazarbayev REUTERS/Piroschka van de Wouw

Majalisar Kasar Kazakhstan ta amince da dokar sauya sunan babban birnin kasar daga Astana zuwa Nursultan domin girmama tsohon shugaban kasa Nursultan Nazarbayev wanda ya sauka daga mukaminsa a jiya Talata bayan kwashe shekaru 30 kan karagar mulki.


Shugaban kasa na riko, Kassym-Jomart Tokayev ya gabatar da bukatar sauya sunan ga majalisar, wadda ba tare da bata lokaci ba ta amince da maatakin.

Har ila yau Majalisar Dokokin Kasar ta amince da 'yar tsohon shugaban Dariga a matsayin shugabar Majalisar Dattawa, bayan shugaban majalisar ya zama shugaban kasa na riko.