Ma'aikatar harakokin wajen Iran ta ce kalaman Trump kan Golan sun harzuka kasar
Ministan harakokin wajen kasar Iran Mohammad Javad Zarif ya bayyana takaicinsa da kalaman shugaban Amruka Donald Trump dake cewa, yana goyon bayan yankin Tundan Golan na Syriya ya zaman mallakain kasar Izra’ila bayan mamaye shi da tayi shekaru 52 da suka gabata.
Wallafawa ranar:
Kasar Iran dai ita ce babbar kawar gwamnatin Bashar al’assad wace ke bashi tallafin soji da tattalin arziki a yakin bsasar kasar ta Syriya
A wani tsokaci da yayi ta shafinsa na Twitter a daura da zaman taron kungiyar kasashen musulmi ta duniya OIC dake gudana a Istambul na kasar Turkiya, a yau ministan harakokin wajen kasar ta Iran ya ce ya ji takaici kan kalaman shugaban na Amruka, dake ci gaba da baiwa Izraela da ya danganta da kasar kabilanci abinda ba mallakinta ba, baya ga birnin Kudus da farko yanzu kuma sai tuddan Golan
A jiya alhamis ne a wani tsokaci da yayi ta shafinsa na Twitter shugaban Amruka ya sake tallabo wata sabuwar, inda yace bayan share tsawon shekaru 52 lokaci yayi da ya kamata Amruka ta amince da hallacin yankin Tuddan Golan ga kasar Israela
Wannan furuci dai ya sake tado jijiyoyin wuyan da dama ke kumbure a yankin gabas ta tsakkiyar
Idan dai ba a manta ba a yakin 1967 Israela ta kama mafi girman yankin na tuddan Golan daga kasar Syriya kafin ta maida shin a cikin kasarta a 1981, to sai dai har kawo yanzu kasashen duniya basu goyi bayan wannan mamayen ba.
Sai dai a 2017, Donald Trump ya karya masalahar dake tsakanin kasashen duniya, inda ya bayyana amincewa da birnin Kudus a matsayin babban birnin kasar Israela.
A’amarin da ya sha tofin Allah Tsine daga kasashen duniya har ma a bangaren kawayen na Amruka
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu