rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

ISIL Syria Iraqi Amurka

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Mun samu cikakkiyar nasarar murkushe ISIS a Syria - SDF

media
Wasu dakarun kungiyar SDF ta hadin gwiwa tsakanin ‘yan tawayen Syria da mayakan Kurdawa da Amurkawa ke marawa baya. AP/Maya Alleruzzo

Rundunar hadakar ‘yan tawayen Syria da mayakan Kurdawa ta SDF da Amurkawa ke marawa baya, ta yi shelar samun cikakkiyar nasarar murkushe mayakan ISIS a kasar ta Syria.


Nasarar na nufin kawo karshen yakin shekaru 4 da mayakan na SDF suka shafe suna gwabzawa da ISIS, kungiyar da ta mamaye yankuna masu fadin gaske a kasar ta Syria da kuma Iraqi.

Da safiyar wannan Asabar kakakin mayakan ‘yan tawayen Syria Mustafa Bali, ya yi shelar samun nasarar ta shafinsa na twitter.

Kafin sanarwar a ranar Juma’a ma’aikatar tsaron Amurka ta bada tabbacin cewa, dakarun hadin gwiwar sun yi nasarar kwace duk wani yanki da a baya ke karkashin ikon kungiyar ta ISIS a Syria.

Kungiyar ISIS ko ISIL reshe ne daga kungiyar al-Qaeda, wadda ta bayyana a kasar Iraqi cikin shekarar 2006, inda ta rika kaiwa sojojin Amurka da kawayensu hare-hare musamman a Bagadaza babban birnin kasar ta Iraqi, shekaru 3 bayan mamaye kasar da sojin Amurka suka yi.

Bayan nasarar korar mayakan ISIL daga Bagadaza sai suka kafa cibiya mai karfi a Mosul, birni na biyu mafi girma a kasar ta Iraqi, inda daga nan kai hare-hare zuwa sauran sassan kasar.

A shekarar 2010, kungiyar ta bayyana Abu Bakr al-Baghdadi a matsayin shugabanta, wanda ya jagoranci hare-hare masu muni kan yankunan Iraqi da Syria, wadanda suka rutsa da fararen hula da dama.