rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Yemen Saudiya Majalisar Dinkin Duniya Gabas ta Tsakiya Hakkin Dan Adam

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Yakin Yemen ya haifar da tagayyarar mutane mafi muni - MDD

media
wasu kanan Yara da yakin Yemen ya raba da muhallansu tare da haramta su ci gaba da zuwa makaranta. BSS/AFP

Majalisar Dinkin Duniya, ta ce Yakin Yemen ya haifar da tagayyarar fararen hula mafi muni a duniya da aka gani a baya bayan nan.


Rahoton Majalisar yace Yakin tsakanin ‘yan tawayen Houthi da dakarun wasu kasashen Larabawa a karkashin jagorancin Saudiya, ya hallaka sama da fararen hula dubu 10, yayinda wasu sama da dubu 60 suka jikkata, sai kuma akalla 'yan kasar miliyan 3 da dubu 300 da suka rasa muhallansu.

Rahoton ya kara da cewa akalla yara yan kasa da shekaru 5, miliyan da 1 dubu 800 ke fama da yunwa a kasar, bayaga wasu dubu 85 da yunwar ta hallaka a tsakanin Afrilu na 2015 zuwa Oktoban 2018.

Zalika a bangaren ilimi, sama da makarantu dubu 2 da 500 ne basa aiki, biyu bisa ukunsu kuma yakin kasar ta Yemen ne ya ragargaza su, hakan tasa kimanin kananan yara miliyan 7 ne basa zuwa makaranta.