rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Syria Majalisar Dinkin Duniya Amurka Isra'ila

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Kwamitin Sulhu ya ki goyon bayan Amurka kan Tuddan Golan

media
Zauren kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya dake birnin New York. REUTERS/Carlo Allegri

A zamansa da ya gudanar a yammacin jiya Laraba, Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya yi watsi da matakin da shugban Amurka Donald Ttump ya dauka, da ke bayyana tsaunukan Golan a matsayin mallakin Isra’ila.


Kwamitin Sulhun yayi watsi da kudurin ne da gagarumin rinjaye, bayan da gwamnatin Syria ta bukaci a gudanar da zama na musamman kan batun.

Ilahirin kasashe 14 mambobin Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya ne suka yi wa Amurka taron dangi tare da yin Allah wadai da kudurin da shugaba Donald Trump ya sanya wa hannu da ke bayyana yankin na Tuddan Golan da Isra’ila ta mamaye da karfi tun 1967 a matsayin wani bangare na kasarta.

Vladimir Safronkov, manzon Rasha a MDD, ya bayyana matakin na Amurka a matsayin wanda ya yu hannun riga da kudurorin da dama na Majalisar, yana mai cewa matakin ba zai iya canza matsayin wannan yanki ba.

A mahawarar da aka tafka yammacin jiya, kasashe mambobi a kwanatin tsaron, ciki har da Beligium, Jamus, Kuweit, China, Indonesoia, Peru, Afirka ta Kudu da kuma Jamhuriyayar Dominican, dukkaninsu sun yi tir da kudurin na shugaba Trump.

To sai dai a lokacin wannan zama, Amurka ta bukaci a ci gaba da barin dakarun wanzar da zaman lafiya na MDD dubu daya a yankin na Tuddan Golan.