rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Afghanistan Taliban

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Mataimakin Shugaban Afghanistan ya ketara rijiya da baya

media
Harin da aka kai zuwa yan Sanda a Afghanistan REUTERS/Omar Sobhani

Mataimakin Shugaban kasar Afghanistan Abdul Rachid Dostom ya ketara rijiya da baya a wani harin kwantar bauna da yan kungiyar Taliban suka kai zuwa ayarin motocin dake tareda shi a arewacin kasar ta Afghanistan.


Lamarin dai ya faru a lardin Balkh dake arewacin kasar,yayinda mai magana da yahun kungiyar Taliban Zabihullah Mijahid ya bayyana cewa kungiyar Taliban ta dau alhakin wannan harin,wanda ya kuma bata damar kashe dogaren mataimakin Shugaban kasar hudu .

Da jimawa yan kungiyar Taliban sun dau alkawalin kisan mataimakin Shugaban kasar ta Afghanistan.