Isa ga babban shafi
Isra'ila

Zanga-zangar Falasdinawa akan iyakar Gaza ta cika shekara 1

Yau Asabar Dubban falasdinawa ke gudanar da gangami a kan iyakar Isra’ila da Yankin Gaza domin bikin cika shekara guda da soma zanga-zanga a kan iyakar, wadda zuwa yanzu sojin Isra'ila suka hallaka Falasdinawa akalla 200 bayan soma gudanar da ita a kowane mako tun daga shekarar bara.

Wasu daga cikin Falasdinawa dake zanga-zanga a kan Isra'ila da yankin Gaza. 29/03/2019.
Wasu daga cikin Falasdinawa dake zanga-zanga a kan Isra'ila da yankin Gaza. 29/03/2019. REUTERS/Mohammed Salem
Talla

A daren jiya Juma’a kungiyar Hamas ta bayyana cimma yarjejeniya da Isra’ila kan cewa Falasdinawa masu zanga-zangar ba za su kusanci jikin katangar da ta raba iyakarsu ba, don kaucewa arrangama tsakaninsu da sojin Isra’ilar, to sai babu tabbacin cimma yarjejeniyar daga hukumomin kasar.

A watan mayu na shekarar bara zanga-zangar ta karfafa, bayanda sojin Isra’ila suka hallaka Falasdinawa 62 a rana guda, lokacin da Amurka ta mayarda ofishin jakadancinta zuwa Birnin Kudus, bisa nufin amincewa da shi a matsayin babban birnin Isra’ila.

Zanga-zangar Falasdinawa na zuwane yayinda ya rage kwanaki 10 Isra’ila ta gudanar da babban zabenta, wanda Fira Minista Benjamin Netanyahu ke neman zarcewa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.