rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Japan Al'adu

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Masarautar Japan na gaf da shiga sabon babi

media
Sakataren majalisar zartaswar gwamnatin kasar Japan Yoshihide Suga yayin bayyana sabon sunan sarautar kasar Japan "Reiwa" a birnin Tokyo. 1/4/2019. AFP/Kazuhiro Nogi

Gwamnatin Japan ta bayyana sauya tushen sunan kasaitacciyar sarautar kasar da ta shafe sama da shekara dubu daya tana wanzuwa.


A karon Farko dai Gwamnatin ta Japan, ta zabo “Reiwa”, wato sunan sarautar daga harshe ko adabinta, a maimakon na kasar China da ta shafe shekara da shekaru tana amfani da shi.

Daga ranar 1 ga watan Mayu mai zuwa, lokacin da Yarima mai Jiran Gado Naruhito zai karbi mulki daga hannun Mahaifinsa Sarkin Japan Akihito, sunan sabuwar sarautar kasar, wato "Reiwa" zai soma aiki.

Ma’anar Sunan Sarautar na "Reiwa" dai shi ne Abu mai kyau da kuma zaman lafiya.

Karon na farko kenan da aka samu irin wannan Sauyi a kasar ta Japan a karkashin mulkin Fira Minista Shinzo Abe, kasancewar sama da shekaru dubu 1,300 kenan da Japan ta ari tsarin mulkin Sarautar gargajiya ta fuskokin suna da kuma Kalanda daga kasar China.

A tsawon shekarun na baya, Japan ta yi amfani da sunaye kashi hudu kan sarautar gargajiyar kasar da suka hada da Maiji, Taisho, Showa sai kuma Heisei, wato kokarin samar da zaman lafiya, wanda yanzu ake kan amfani da shi, amma daga ranar 30 ga watan Afrilu da muke ciki, za’a maye gurbin sunan sarautar da "Reiwa".