rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Afghanistan Taliban

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Wakilan Afghanistan 250 za su gana da wakilan Taliban a Doha

media
Wakilan kungiyar Taliban a ganawarsu da wakilan Amurka domin tattaunawar sasanta rikicin kasar Afghanistan a birnin Doha na Qatar Qatari Foreign Ministry/Handout via REUTERS

Gwamnatin Kasar Afghanistan ta bayyana jerin sunayen wakilan ta da za su gana da wakilan kungiyar Taliban a taron sasanta rikicin kasar da zai gudana a Doha a cikin wannan mako.


Jerin sunayen wakilan gwamnatin 250 da fadar shugaban kasa ta gabatar, ya sanya sunayen babban hafsa a fadar shugaban kasa Ashraf Ghani, wato Abdul Salam Rahimi da Amrullah Salah, tsohon shugaban hukumar liken asiri.

A baya dai kungiyar Taliban ta ki ganawa da wakilan gwamnati yayin da ta ke tattaunawa da wakilan gwamnatin Amurka kan kawo karshen yakin kasar.