Isa ga babban shafi
Srilanka

Sri Lanka ta fara makokin mutum 310 da jerin harin bom ya hallaka

Dubban Al’umma a Sri Lanka sun halarci makokin mutanen da suka rasa rayukansu a hare-haren bom din da suka faru ranar Lahadi, dai dai lokacin da gwamnatin kasar ta ayyana makokin rana guda don jimamin mutanen da suka rasa rayukansu.

Dubban al'ummar Sri Lanka ne dai suka halarci zaman jana'izar da ya gudana a Negombo
Dubban al'ummar Sri Lanka ne dai suka halarci zaman jana'izar da ya gudana a Negombo REUTERS/Thomas Peter
Talla

Makokin dai na zuwa ne dai dai lokacin da rundunar ‘yan sandan kasar ta Sri Lanka ke cewa adadin wadanda harin ya hallaka ya karu zuwa Mutum 310.

Tuni dai ilahirin al’ummar kasar suka gudanar da wani zaman shiru na mintuna 3 don jimamin wadanda suka mutu a harin, yayinda gwamnati ta sanar da daukar matakan kaucewa sake faruwar harin a nan gaba.

Gwamnatin kasar ta Sri Lanka dai ta dora alhakin harin kan wata kungiyar ta’addanci ta Thowheed Jamath wato NTJ inda kwao yanzu jami’an tsaro suka kame mutane 40 wadanda ake zargi da hannu a kitsa harin.

An dai gudanar da janazar mutanen a majami’ar St Sebastian da ke Negombo a arewacin Colombo, guda cikin Majami’un da suka fuskanci hare-haren na ranar Lahadi.

Haka zalika zaman shirin na mintuna 3 ya fara ne da misalin karfe 8:30 na safiyar yau, dai dai lokacin da Bom din farko ya tashi a kasar ranar Lahadi.

Kafafofin yada labarai dai sun nuno miliyoyin al’ummar ta Sri Lanka duke da kawuna a kasa don girmama mintunan 3 tare da jimamin wadanda suka mutu dama fiye da mutane 500 da suka jikkata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.