rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Japan Faransa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Carlos Ghosn ya bar gidan yarin birnin Tokyo

media
Carlos Ghosn, tubabben shugaban kamfanin Renault-Nissan. REUTERS/Regis Duvignau/File Picture

Tsohon shugaban kamfanin Nissan Carlos Ghosn ya bar gidan yarin da ake tsare da shi a wannan alhamis,. Bayan da kotu ta amince ya biya kudin beli dalar Amurka milyan  4 da dubu 500.


Ghosn mai shekaru 64 a duniya, an cafke shi ne bisa zargin aikata laifufuka guda hudu da suka shafi yin facaka da dukiyar kamfanin wanda ke hadin gwiwa da wasu manyan kamfanonin kera motoci da suka hada da Mitsubishi da kuma Renault.

To sai dai bayan sallamar sa daga gidan yari a wannan alhamis, kotu ta gindayawa Carlos Ghosn wasu sharudda ciki har da hana shi yin tozali da matarsa.