Isa ga babban shafi
Saudiyya

Ana taron kasashen musulmi da na Larabawa a Saudiyya

Shugabannin kasashen musulmi da na Larabawa sun isa bisa birnin Makka a yau alhamis, domin gudanar da taruruka uku mabambanta, a cikin wani yanayi da Saudiyya ke neman samun goyon bayan sauran kasashe biyo bayan harin da aka kai wa cibiyoyinta na man fetur.

Ministocinn wajen kasashen yankin Gulf, a taronsu na birnin Riyadd, 7,disamba 2015
Ministocinn wajen kasashen yankin Gulf, a taronsu na birnin Riyadd, 7,disamba 2015 REUTERS/Faisal Al Nasser
Talla

Da farko dai an shirya gudanar da taron kungiyar kasashen musulmi ta OIC ne a birnin na Makka, kafin daga bisani Saudiyya mai masaukin baki ta kira taron kungiyar kasashen Larabawa da kuma na kasashen yankin Tekun Fasha.

Saudiyya na zargin Iran da taimaka wa wadanda ke neman kawo cikas ga ayyukan hakar man fetur a kasarta, bayan da ‘yan tawayen Huthi da ke Yemen suka yi amfani da wani jirgi mai sarrafa kansa domin kai hari a kan bututun mai mallakin kasar, yayin da a daya bangare aka kai hari kan jiragen ruwan dakon man fetur a tekun Fasha, laifufukan da ake dangantawa da Iran.

Har ila yau taron na gudanar da ne a daidai lokacin da ake zaman tankiya tsakanin Amurka, kasashen yankin Gulf da kuma Iran.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.