rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Philippines Canada

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

philippines ta mayar da shara zuwa Canada

media
Shara a kasar Philippines J Gerard Seguia/SOPA Images/LightRocket via Getty Images

Philipines ta mayar da dimbim ton na shara da aka kwaso daga Canada a shekaru da dama da suka wuce zuwa Canadan a yau Juma’a, bayan wani rikicin diflomasiya mai zafi, a dai-dai lokacin da kasar ta yankin Asiya ke ci gaba da yin turjiya game da maida ta wajen zuba shara daga kasashen waje.


Bayan wani kokari da ta dade tana yi na kira ga Canadan ta kwashe sharar da ta jibge mata, shugaban Philipines Rodrigo Duerte ya caccaki Canadan a makon da ya gabata, kana ya umarci da a mayar da sharar ba tare da bata lokaci ba.

A wannan lokaci kungiyoyi dake yaki da gurbacewar yanayi sun bayyana farin cikin su a wannan mataki ,wanda shaka babu zai tilastawa Canada daukar matakan kula da kuma tsaptace muhalin ta ga baki daya.