Isa ga babban shafi
China

China ta yi bikin cika shekaru 30 da kazamin boren Tiananmen

China ta yi bikin cika shekaru 30 da aukuwar kazamin boren jama’a suka yiwa gwamnati a katafaren filin taro na Tiananmen da ke birnin Beijing.

Sojin kasar China yayin gadin filin taro na Tiananmen da ke birnin Beijing a watan Yuni na shekarar 1989, bayan kazamin boren masu neman komawa tsarin dimokaradiyya da sojoji suka murkushe.
Sojin kasar China yayin gadin filin taro na Tiananmen da ke birnin Beijing a watan Yuni na shekarar 1989, bayan kazamin boren masu neman komawa tsarin dimokaradiyya da sojoji suka murkushe. AFP/CATHERINE HENRIETTE
Talla

A waccan lokacin dai sai da jami’an tsaro suka yi amfani da karfi wajen murkushe boren na masu fafutukar ganin China ta koma bin tsarin Dimokaradiyya daga na gurguzu.

A ranar 4 ga watan Yuni na shekarar 1989 dubban jama’a suka tayar da kazamin boren a filin taron na Tiananmen, har sai da sojoji suka yi amfani da tankunan yaki wajen murkushe boren, lamarin da yayi sanadin hallakar sama da mutane dubu 1.

Yayin bikin na yau dai, jami’an tsaron China sun haramtawa manema labarai na kasashen ketare da dama shiga cikin filin taron na Tiananmen, yayinda wasu yan jaridun aka hana su daukar hotuna.

Bikin tunawa da zagayowar ranar gagarumin Boren na Tiananmen da Amurka ta yi tsokaci akai na nuna goyon bayan ga ‘yan kasar ta China masu fafutukar komawa tsarin Dimokaradiya, ya zo ne a dai dai lokacin dagantaka ta yi tsami tsakanin Amurkan da China sakamakon rikicin kasuwancin da suka shafe watanni suna yi.

A Hong Kong, yankin da ya koma karkashin mulkin China a 1997, amma tare da amfana da wani mataki na yancin cin gashin kansa, dubban jama’a da ke goyon bayan samun cikakken yanci, sun gudanar da nasu taron na tunawa da boren na Tiananmen, da kuma alhinin wadanda suka rasa rayukansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.