Isa ga babban shafi
Hong Kong

Dokar tasa keyar masu laifi zuwa China na nan daram

Shugabar Gwamnatin Hong Kong Cariie Lam ta bayyana cewa, ba za ta soke dokar tasa keyar masu laifi zuwa China don fuskantar hukunci ba, duk da zanga-zangar adawa da wannan mataki.

Dubban jama'ar Hong Kong sun gudanar da zanga-zangar adawa da dokar tasa keyar masu laifi zuwa China daga Hong Kong
Dubban jama'ar Hong Kong sun gudanar da zanga-zangar adawa da dokar tasa keyar masu laifi zuwa China daga Hong Kong REUTERS/Thomas Peter
Talla

A ranar Lahadin da ta gabata ne, dubban jama’ar Hong Kong suka gudanar da gagrumin gangamin nuna adawa da kudirin dokar wanda masu sukar tsarin ke cewa, zai bai wa China damar yi wa ‘yan adawarta bita da kullin siyasa.

Sai dai a yayin zantawa da manema labarai a wanan Litinin, Uwargida Lam ta hakikance cewa, akwai bukatar kafa dokar, yayinda kuma ta ce, za a kare hakin bil’adama.

Kafofin yada labaran kasar China sun bayyana cewa, wasu kasashen waje ne suka tunzura gudanar da zanga-zangar adawa da matakin.

Rahotanni sun ce, akalla mutane miliyan 1 ne suka fantsama kan tituna domin shiga zanga-zangar ta karshen mako. Kodayake jami’an ‘yan sanda sun musanta adadin, inda suka ce, masu zanga-zangar basu wuce dubu 240 ba.

Ana sa ran gudanmar da wata sabuwar zanga-zanga a ranar Laraba mai zuwa, lokacin da Majalisar Dokokin Hong Kong za ta yi zaman karatu na biyu kan kudirin dokar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.