rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Philippines Hakkin Dan Adam

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Iceland ta bukaci hukunta Duterte bisa halaka mutane dubu 27

media
Shugaban kasar Philippines Rodrigo Duterte. © Reuters

Yan siyasa da kungiyoyin fararen hula a Philippines, sun goyi bayan kudurin da ya bukaci majalisar dinkin duniya, ta dauki mataki kan gwamnatin shugaban kasar Rodrigo Duterte, bisa dubban mutanen aka kashe da sunan yaki da masu tu’ammuli da miyagun kwayoyi.


Kasar Iceland ce dai ta gabatarwa hukumar kare hakkin dan adam ta majalisar dinkin duniya, bukatar bincikar gwamnatin Duterte, da ake zarginta da halaka mutane akalla dubu 27, bayan kaddamar da yaki miyagun kwayoyi.

Zuwa yanzu kasashe 28 ne suka goyi bayan kudurin, mafi akasarinsu na Turai, inda kuma ake sa ran a ranar 12 ga watan Yuli, manbobin hukumar kare hakkin ta duniya za su kada kuri’a akai.

A shekarar bara kotun duniya ICC ta kaddamar da bincike kan shugaban kasar ta Philippines Rodrigo Duterte dangane da yakar tu’ammuli da miyagun kwayoyi da ya kaddamar a watan Yuli na shekarar 2016.