Isa ga babban shafi
Amurka- Iran

Iran ta yi barazanar ci gaba da bijirewa yarjejeniyar nukiliyar 2015

Sa’o’I kalilan bayan da ta kara yawan sinadaran uranium din da ta ke tacewa a karo na biyu zuwa kashi 5, kasar Iran ta yi barazanar ci gaba da karya sauran ka’idojin da yarjejeniyar nukuliyar tata ta kunsa matukar ba a kai ga matakin sasantawa tsakaninta da Amurka ba, cikin kwanaki 60 masu zuwa.

Shugaban kasar Iran Hassan Rohani
Shugaban kasar Iran Hassan Rohani HO / IRANIAN PRESIDENCY / AFP
Talla

Tun ranar 8 ga watan Mayun da ya gabata ne, shekara guda cif bayan ficewar Amurka daga yarjejeniyar, shugaban Iran Hassan Rouhani ya fara barazanar karya ka’idodjin yarjejeniyar, matakin da ya haddasa cecekuce tsakanin kasar da sauran manyan kasashen duniya da suka kulla yarjejeniyar a 2015.

Cikin kalaman Behrouz Kamalvandi mai Magana da yawun sashen makamashin kasar ta Iran, a jawaban da ya gabatar kai tsaye ta gidan talabijin ya tabbatar da cewa yanzu haka Iran ta fara tace kashi biyar na sinadarin Uranium.

Shima mataimakin ministan wajen kasar Abbas Aragchi, ya ce suna kan hanyar ci gaba da karya wasu ka’idoji da yarjejeniyar ta kunsa nan da kwanaki 60 masu zuwa, ko dai bai bayyana hakikanin matakin da kasar ke shirin dauka ba.

Tuni dai kasashen da ke cikin yarjejeniyar ciki har da Birtaniya da Jamus suka bukaci Iran ta gaggauta dakatar da dukkan tsare-tsarenta da ke kokarin yiwa yarjejeniyar nukuliyarta karan tsaye, sa’o’i kalilan bayan Tehran ta bayarda wa’adin kwanaki 60 kafin ci gaba karya ka'idojin yarjejeniyar ta shekarar 2015.

Ofishin harkokin wajen Birtaniya ya fitar da sanarwar da ke nuna cewa, kasar na ci gaba da mutuntawa tare da tsare ka’idodjin yarjejeniyar, a don haka babu hujjar da zai sanya Iran ficewa daga cikinta.

A cewar sanarwar Birtaniya na aiki tare da sauran kasashe 5 da suka kulla yarjejeniyar wajen ganin ta ci gaba da dorewa tare da lalubo hanyoyin magance rikicin da ya kunno kai tsakanin Tehran da Washington.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.