rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Yemen

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

An kashe 'yan sandan Yemen a harin ta'addanci

media
Wasu daga cikin jami'an tsaron Yemen a wurin da aka kai harin ta'addancin a birnin Aden REUTERS/Fawaz Salman

Akalla mutane 27 sun rasa rayukansu da suka hada da jami’an ‘yan sanda sakamakon wasu tagwayen hare-hare da ‘yan tawayen Houthi da kuma mayakan jihadi suka kaddamar a birnin Aden na kasar Yemen.


A karon farko kenan a cikin sama da shekara guda, da ake kaddamar da hare-haren a birnin Aden mai tashar jiragen ruwa, lamarin da ake kallo a matsayin gagarumin koma-baya ga jami’an tsaron Yemen da suka samu horo na musamman da tallafin kayayyakin soji daga Hadaddiyar Daular Larabawa.

Mayakan jihadi sun kai farmakin farko ne kan jami’an ‘yan sanda kamar yadda majiyoyin tsaro suka tabbatar, in da mutane 10 cikinsu har da ‘yan sanda uku suka riga mu gidan gaskiya nan take, yayinda kuma 20 suka jikkata.

Mayakan Houthi ne suka kaddamar da hari na biyu, inda suka ce sun yi amfani da jirgin sama mara matuki da makami mai linzami wajen kai harin a sansanin horar da ‘yan sanda a yammacin birnin Aden.

Akalla ‘yan sanda 17 ne suka mutu a farmakin na biyu, yayinda gommai suka jikkata.

Harin na ‘yan tawayen Houthi ya dirar wa jami’an ‘yan sandan ne a daidai lokacin da wasu manyan kwamadojinsu ke kallon faretin kammala makarantar horar da kananan ‘yan sanda.

Harin dai ya yi sanadin mutuwar guda daga cikin manyan kwamandojin na ‘yan sandan Yemen.