rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Yemen

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Adadin mutanen da suka halaka a hare-haren Yemen ya karu

media
Bangaren sansanin jami'an tsaron Yemen na Al-Jala dake yammacin birnin Aden da 'yan tawayen Houthi suka kaiwa farmaki. AFP / Nabil HASAN

Hukumomin Kasar Yemen sun ce adadin mutanen da suka mutu sakamakon hare-haren da mayakan Houthi suka dauki alhakin kaiwa a birnin Aden ya kai 49, yayin da wasu da dama suka jikkata.


Hare-haren su ne na farko a garin dake dauke da tashar jiragen ruwa, a cikin shekara guda, matakin dake nuna gazawar matakan tsaron da gwamnatin kasar ke dauka.

Mohammed Rabid, babban jami’in ma’aikatar lafiya, yace bayan mutane 49 da suka mutu, wasu 48 sun jikkata.

Mai magana da yawun kungiyar Yan Tawayen Houthi ya bayyana cewar sun kai harin ne da wani makamin da basu saba amfani da shi ba, da kuma jirgi mai sarrafa kan sa.