rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Pakistan India

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Pakistan ta yanke duk wata hulda da makociyarta India

media
Firamininstan Pakistan Imran Khan ALEXEY DRUZHININ / SPUTNIK / AFP

Pakistan ta kori jakadan India daga kasar, tare kuma da yanke dukkanin wata huldar kasuwanci da Diflomasiyar da ke tsakanin kasashen biyu makotan juna.


Pakistan ta dauki matakin ne domin maidawa India martani, kan soke kwarya-kwaryar 'yancin cin gashin kan yankin Kashmir da ta yi, yankin da kasashen biyu suka kwashe shekaru da dama suna rikici kan mallakarsa.

Tun a Asabar din da ta gabata ne, India ta yi barazanar cewa akwai bayanan sirri da ke nuna yiwuwar kai hari yankin na Kashmir matakin da ya tilastawa daruruwan 'yan yawon bude ido ficewa daga yankin.

Haka zalika a shekaran jiya Litinin, India ta fara tattaunawa kan batun kwace kwarya-kwaryar 'yancin cin gashin kan yankin matakin da ya sanyawa dubun-dubatar jama'a gudanar da zanga-zanga tare da kalubalantar matakin musamman a kan iyakokin kasar.

Tsawon shekaru dai kasashen biyu na rigima da juna kan yankin na Kashmir mai rinjayen mabiya addinin Islama.