rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Hong Kong China

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

An soke tashi da saukar jiragen sama a Hong Kong

media
Mazu zanga-zanga a filin sauka da tashin jiragen saman Hong Kong RFI/Christophe Paget

An soke sauka da tashin jiragen sama baki daya daga a Hong Kong, sakamakon yadda masu rajin kare dimokuradiyya suka mamaye filin jirgin saman a wannan litinin.


Hong Kong, a can ne ake da daya daga cikin manyan filaye jiragen sama a duniya, wanda masu tarzomar suka mamaye a daidai lokacin da suka cika makonni 10 suna zanga-zangar kin jinin shugabar gwamnatin yankin mai kwarya-kwaryan ‘yancin cin gashin kai.

Kafin tsakiyar rana, akalla mutane dubu biyar ne suka kutsa kai a cikin filin jirgin saman yayin da wasu dubbai suka yi cincirindo a waje dukanninsu dauke allunan da aka rubuta kalmomin yin tir da abin da suka kira mulkin kama karya, yayin da wasu ke jaddada kir aga shugabar gwamnatinsu ta yi marabusu.