rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Iran Birtaniya Syria Gabas ta Tsakiya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Kotun koli ta umurci Birtaniya ta saki jirgin ruwan Iran da ta kame

media
Jirgin ruwan dakon man fetur na Iran da Birtaniya ta kame cikin watan Yuli. AFP / Jorge Guerrero

Kotun kolin tsibirin Gilbratar, ta bayar da umurnin sakin jirgin dakon man fetur na Iran da Birtaniya ta kama tun ranar 4 ga watan yulin da ya gabata.


Birtaniya dai ta ce ta kama jirgin ne, bisa zargin cewa yana kan hanyar zuwa kasar Syria, duk da cewa a karkashin kudurorin majalisar dinkin duniya an haramta shigar da mai zuwa kasar mai fama da yakin basasa yau shekaru 8.

Tun da fari dai farko Amurka ce ta bukaci kotun ta bayar da umurnin kwace jirgin ruwan dakon man, sai dai ministann shari’a a tsibirin na Gilbratar Fabian Picardo ya ce ba hujjar ci gaba da tsare jirgin.

Ministan harkokin wajen kasar Iran Mohammed Javad Zarif ya ce hukuncin kotun wani mummunan koma-baya ne ga yunkurin da Amurka ta yi na fashin wannan jirgi a kan teku.

Bayan kama wannan jirgi mallakin Iran, an shiga takun saka tsakanin kasar ta Iran da wasu kasashe na aminan Amurka, inda bisani kasashen suka yanke shawarar kafa runduna ta musamman domin rakiyar jiragen da ke ratsa mashigin ruwan Hormoz.