rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya
  • Palestinawa 22 hare-hare daga Israela ya kashe a Gaza.
  • Dan kunar bakin wake ya kashe mutun daya a ofishin 'yan sandan Indonesia

Afghanistan Taliban Amurka Ta'addanci

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Afghanistan: IS ta dauki alhakin harin bam din da ya halaka mutane 63

media
Wani bangare na filin taron bikin daurin auren da aka kaiwa harin bam a Kabul, babban birnin Afghanistan. REUTERS/Mohammad Ismail

Kungiyar IS ta dauki alhakin mummunan harin bam din da ya halaka mutane 63, tare da jikkata wasu 182, a wajen taron daurin aure a Kabul, babban birnin kasar Afghanistan.


Kungiyar ta IS tace wani mayakinta ne ya tarwatsa bam din da ke jikinsa, yayinda ake tsaka da bikin, harin da hukumomin kasar suka ce shi ne mafi muni a baya bayan nan.

Harin ya zo ne a dai dai lokacin da wakilan mayakan kungiyar Taliban da Amurka ke gaf da cimma yarjejeniyar kawo karshen yakin kusan shekaru 18 da suke gwabzawa, matakin da zai bada damar janye dubban dakarun Amurkan dake kasar ta Afghanistan.

Tuni dai kungiyar Taliban ta nesanta kanta daga harin.