rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Hong Kong China

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Hong Kong: Masu zanga-zangar na fatan tara mutane sama miliyan 1

media
Dubban masu zanga-zangar adawa da China a yankin Hong Kong. 18/8/2019. Philip FONG / AFP

Dubban masu zanga-zanga a Hong Kong sun yi fitar dango kan titunan birnin, domin nunawa hukumomin yankin da kasar China gagarumin goyon bayan da suke da shi, kan aniyarsu ta neman karin 'yanci daga China, da kuma komawa kan tsarin dimokaradiya irin na Turai.


Zanga-zangar ta Hong Kong da ake saran za ta tara mutane sama miliyan daya, na gudana ne, duk da haramta ta da ‘yan sandan yankin suka yi, da kuma gargadin gwamnatin China.

Zuwa yanzu an shafe sama da makwanni 10 dubban masu zanga-zanga na gangami a Hong Kong, zanga-zangar da ta samo asali daga adawa da dokar mika masu laifi daga yankin zuwa China domin fuskantar hukunci.

A makon daya kare ne China ta yi tur da masu zanga-zangar a Hong Kong tare da kamanta su da ‘yan ta’adda, bayan da suka gurgunta filin jiragen saman yankin tsawon sa'o'i.