Isa ga babban shafi

Japan na karbar bakoncin taron bunkasa nahiyar Afrika

Shugabannin kasashen Afirka sun fara hallara a birnin Yokohama na Japan, don halartar babban taron bunkasa nahiyar, wadda za a fara daga ranar 28 zuwa 30 ga wannan watan da muke ciki.

Shugaban kasar Japan Shinzo Abe
Shugaban kasar Japan Shinzo Abe REUTERS/Issei Kato
Talla

Gwamnatin Japan ce za ta jagoranci wannan taro, tare da hadin gwiwar Majalisar Dinkin Duniya, da Hukumar bunkasa kasashe ta Majalisar baya ga Bankin Duniya da kuma kungiyar Tarayyar Afirka.

Daga cikin shugabannin kasashen Afirka da za su halarci taron, akwai shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya, Cyril Ramaphosa na Afirka Ta Kudu, Ibrahim Boubacar Keita na Mali, Edgar Lungu na Zambia da Macky Sall na Senegal.

Taro ne na kasa da kasa da ke mayar da hankali kan bunkasar nahiyar Afirka, wadda Japan ta kaddamar a shekarar 1993, kuma ake gudanarwa duk bayan shekaru biyar har zuwa shekarar 2016 da aka fara gudanar da shi duk bayan shekaru uku, a lokacin ne ma aka gudanar da shi a birnin Nairobin Kenya.

Baya ga tattauna ainihin maudu’in taron da shugabannin kasashen Afirka da wakilai za su yi, akwai kananan taruka da aka shirya don kasashen su tattauna da kasar da ta karbi bakuncin taron.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.