rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

India Diflomasiya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Sama da mutane milyan daya zasu rasa asalin su

media
Wasu daga cikin yankunan Assam da aka gudanar da wannan kidaya REUTERS/Mukesh Gupta

Akala mutane milyan biyu ne za su rasa asalin su ko takardar dan kasa a Indiya a yankin Assam dake arewa maso gabacin kasar.

Wannan na zuwa ne bayan kidayar mazaunan yankunan Assam daga jami'an gwamantin kasar ta India.


Akasarin mutanen da wannan mataki ya shafa ,an bayyana cewa musulmai ne, biyo bayan rijista na tattance jama’a.

Kidayar mutanen da aka yi  ya kai akala milyan 31 da yan kai a wannan yankin na Assam.

Yan Sanda sun karfafa matakan tsaro biyo bayan sakamako na wannan kidaya da aka yi a yankin na Assam.

Wasu daga cikin kungiyoyin kare hakokin bil Adam na danganta wannan kidaya  a matsayin abinda ya sabawa dokokin bil Adam ganin sharrudan da ake bukata kowane daga cikin mutanen yankin ya gabatar domin tabbatar da cewa dan kasar India ne.