Isa ga babban shafi
Asiya

Zanga-zangar yankin Hong Kong ta sake kazanta

Zanga-zangar da dubun dubatar al'ummar yankin Hong Kong suka shafe sama da makwanni 14 suna yi, ta adawa da gwamnatinsu da kuma China ta kazanta a wannan asabar, inda jami’an tsaro da masu zanga-zangar suka yi arrangama.

Jami'an tsaron yankin Hong Kong cikin shirin ko ta kwana.
Jami'an tsaron yankin Hong Kong cikin shirin ko ta kwana. © Reuters
Talla

Gungu-gungu na masu zanga-zangar sun kafa shingaye, tare da kunna wuta kan tituna, gami da jifan ‘yan sanda da kwalabe, yayinda su kuma jami’an tsaron suka maida raddi ta hanyar feshin wuta da harba hayaki mai sa hawaye.

Kudurin dokar mika masu lafi daga yankin na Hong Kong zuwa China ne dai ya soma haddasa gagarumar zanga-zangar, wadda a yanzu ta rikide zuwa ta neman komawar yankin kan tsarin Dimokaradiyya irin na Turai, da samun karin yanzi daga China.

A ranar Juma'a Kungiyar Tarayar Turai ta bayyana rashin amincewa da kamen da hukumomin Hong Kong ke yiwa masu rajin kare dimokradiya, yayinda mahukuntan China suka jaddada cewa sam babu zancen lallashin masu bore da ake yi.

Uwargida Federica Mogherini, mai magana da yawun kungiyar kasashen na Turai ta  bukaci ganin mahuntan Hong Kong ta mutunta ‘yancin fadin albarkacin baki, da ‘yancin gudanar da taro.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.